Rahotanni: An Kai Gungun Hare-Haren Ta'addanci Birnin London
Rahotanni daga birnin London na kasar Birtaniyya sun bayyana cewar an kai wasu jerin hare-hare a birnin na London a daren jiya da yayi sanadiyyar mutuwa da kuma raunana wasu mutane lamarin da 'yan sanda da kuma jami'an kasar suka bayyana da cewa wani hari ne na ta'addanci.
Rahotannin sun ce lamarin ya faru ne a daren jiya Asabar lokacin da wasu mutane cikin wata babbar motar daukar kaya suka nufi hanyar da mutanen masu tafiya a kasa suke bi a kan 'Gadar London wadda ke tsakiyar birnin inda suka ta banke mutane lamarin da yayi sanadiyyar mutuwar alal akalla mutane 6 da kuma raunana wasu kimanin 30.
Har ila yau rahotannin sun ce daya daga cikin mutanen cikin motar, wasu kuma sun ce direbar motar ya fito inda ya dinga caccaka wa mutane wuka da kuma wasu da suke wata kasuwa ta Borough Market.
Tuni dai 'yan sanda da sauran jami'an tsaron Birtaniyyan suka sanar da daukar tsauraran matakan tsaro a birnin kamar yadda kuma aka sanar da cewa ana neman wasu mutane uku da ake zargin suna da hannu cikin wannan harin.
Wannan harin dai ya zo ne bayan wasu kwanaki da wani hari da aka kai birnin Manchester na Ingilan da yayi sanadiyyar mutuwar sama da mutane 20 da raunana wasu da dama.