Jun 08, 2017 11:54 UTC
  • Fashewar Bam A Ofishin Jakadancin Amurka Dake Kasar Ukreine

Jami'an 'yan sandar kasar Ukreine sun sanar da fashewar Bam a Ofishin Jakadancin Kasar Amurka dake birnin Kiev

Tashar Telbijin din Alhadas  ta kasar Saudiya ta nakalto jami'an 'yan sandar kasar Ukreine a wannan Alkhamis na cewa wani mutum da ba a kai ga gane ko waye ba ya jeba Bam a ofishin Jakadancin kasar Amurka dake birnin Kiev fadar milkin kasar.

Jami'an 'yan sandar sun tabbatar da cewa harin na ta'addanci ne, amma kuma babu wani da ya rasa ransa dangane da fashewar Bam din, amma dangane da mutanan da suka jikkata har yanzu ba a bayar da wani cikekken bayyani ba.

Tuni dai Gwamnatin kasar ta yi alawadai da wannan hari, inda ta bayyana shi a matsayin harin ta'addanci.

Tags