Theresa ta Nemi Gafarar Wakilan Jam'iyarta A Majalisa
(last modified Sat, 10 Jun 2017 11:53:18 GMT )
Jun 10, 2017 11:53 UTC
  • Theresa ta Nemi Gafarar Wakilan Jam'iyarta A Majalisa

Firaministar Birtaniya Theresa May ta nemi gafarar wakilan Jam'iyarta dake Majalisar dokokin kasar biyo bayan shan kayin da jam'iyar su ta yi a zaben 'yan Majalisun da aka gudanar

Tashar Telbijin CNN ta nakalto Theresa May Firaministar Birtaniya kuma Shugabar jam’iyyar masu ra’ayin rikau tana neman gafarar 'yan Majalisar Dokokin kasar da suka rasa kujerunsu kalkashin Jam'iyyar.

Tun bayan zaben jin ra'ayin Al'ummar na fitar kasar daga cikin kungiyar kasashen Turai,Theresa May ta karbi jagoranci jan ragamar kasar ta Birtaniya inda ta yi alkawarin gudanar da milki duk da irin mawuyacin halin da kasar ke ciki.

Babban fatan Theresa da magoya bayanta dangane da wannan zabe dai shi ne samun cikakken rinjaye a majalisar ba tare da ta nemi kulla kawance da wasu jam’iyyun siyasa ba, kuma ta haka ne wadanda suka jagoranci gwagwarmayar ballewar kasar daga Turai za su iya aiwatar da manufofinsu a siyasance.

A zaben ranar Alkhamis din da ta gabata babu wata jam'iya da ta samu kujeru 326 daga cikin kujeru 650 da Majalisar Birtaniyar ke da ita.