Faransa : Jam'iyyar Shugaba Macron Na Kan Gaba A Zaben Majalisar Dokoki
https://parstoday.ir/ha/news/world-i21244-faransa_jam'iyyar_shugaba_macron_na_kan_gaba_a_zaben_majalisar_dokoki
Rahotanni daga Faransa na cewa jam'iyyar shugaba Emanuelle Macron da jami'yyar MoDem dake kawance da ita na kan gaba da rinjaye a zaben yan majalisar dokokin kasar zagaye na farko da aka kada kuri'arsa a jiya Lahadi.
(last modified 2018-08-22T07:00:14+00:00 )
Jun 12, 2017 01:14 UTC
  • Faransa : Jam'iyyar Shugaba Macron Na Kan Gaba A Zaben Majalisar Dokoki

Rahotanni daga Faransa na cewa jam'iyyar shugaba Emanuelle Macron da jami'yyar MoDem dake kawance da ita na kan gaba da rinjaye a zaben yan majalisar dokokin kasar zagaye na farko da aka kada kuri'arsa a jiya Lahadi.

Sakamakon karshen da aka fitar ya nuna cewa jam'íyyar ta Macron ta samu kashi 32,32% na yawan kuri'un da aka kada, inda take gaban jam'iyyar masu tsattsauran ra'ayi ta conservatives, wadda ke da yawan kuri'un kashi 21,56%.

Sai kuma jam'iyyar National Front mai fatan kafa kawancen 'yan adawa data samu kaso 13,20%, yayin da jam'iyya mai barin gado ta Socialist ke da kaso 9,51% na daukacin kuri'un da aka kada.

Bisa jimillar sakamakon farko da aka tattara, ga alama LREM da kawayen ta, za su lashe kimanin kujerun wakilcin kujeru 400 zuwa 455, cikin jimillar kujerun majalissar dokokin kasar 577.