An Samu Sabani Dangane Da Rikicin Qatar A Gwamnatin Amurka
(last modified Mon, 12 Jun 2017 11:20:58 GMT )
Jun 12, 2017 11:20 UTC
  • An Samu Sabani Dangane Da Rikicin Qatar A Gwamnatin Amurka

Akwai Sabani Tsakanin Saktaren Harakokin Waje da Ministan Tsaro na Gwamnatin Amurka Dangane da Rikicin Kasar Qatar

Tashar Telbijin din CBS News ta nakalto David Ignatius wani mai sharhi kan harakokin Siyasar Amurka na cewa Ministan tsaron Amurkan na fargabar makomar Sojojin kasar dake jibke a babban sansanin kasar Qatar na Al-Aded dake yankin Tekun Fasha, kuma sansanin na mahimancin gaske a yaki da 'yan ta'addar IS.

A nasa bangare Shugaban kasar ta Amurka Donal Trump na ganin cewa wannan wata dama ce ta samu na tilastawa kasar Qatar ta kawo karshen goyon bayan da ake baiwa masu tsautsauran ra'ayin Addini. 

A Halin da ake ciki akwai sama da Sojojin Amurka dubu goma sha daya a sansanin Soja biyu dake cikin kasar ta Qatar.