Tsananta Dokokin Kudin Turai Bayan Ficewar Kasar Birtaniya
(last modified Tue, 13 Jun 2017 11:21:13 GMT )
Jun 13, 2017 11:21 UTC
  • Tsananta Dokokin Kudin Turai Bayan Ficewar Kasar Birtaniya

Za A tsananta dokokin Kudin kasashen Turai bayan ficewar kasar Birtaniya daga cikin kungiyar

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya nakalto Shugaban Kwamitin kungiyar Tarayyar Turai Valdis Dombrovskis a wannan talata na cewa an samar da wasu sabin dokokin da suka shafi harakokin shige da fice na kudaden kungiyar Tarayyar Turai, nan ba da jimawa ba za a zartar da su bayan gudanar da gyare  gyare da suka dace daga kasashen manbobin kungiyar da kuma Majalisar kungiyar Tarayyar Turai.

Babban abinda dokokin suka fi mayar da hankali, ramuwar hasarar da kasashen suka yi bayan ficewar Birtaniya daga kungiyar Tarayyar Turai, da farfado da tattalin arzikin kungiyar ta hanyar karbar riba mai yawa na shige da ficen kudin Euro.