Faransa : Valls, Ya Fice Daga Jam'iyyar 'Yan Gurguzu
https://parstoday.ir/ha/news/world-i21692-faransa_valls_ya_fice_daga_jam'iyyar_'yan_gurguzu
Tsohon fira ministan Faransa, Manuel Valls, ya sanar da ficewarsa daga jami'iyar 'yan gurguzu ta 'socialist'.
(last modified 2018-08-22T07:00:18+00:00 )
Jun 27, 2017 05:37 UTC
  • Faransa : Valls, Ya Fice Daga Jam'iyyar 'Yan Gurguzu

Tsohon fira ministan Faransa, Manuel Valls, ya sanar da ficewarsa daga jami'iyar 'yan gurguzu ta 'socialist'.

Mista Valls ya sanar a gidan radiyo na RTL cewa ''yau wani bangare na rayuwar siyasata ya kawo karshe, na bar jam'iyyar 'yan gurguzu, ko kuma jam'iyyar ta barni''.

Valls dai she tsohon fira ministan shugaban jam'iyar 'yan gurguzu tsohon shugaba Farancois Hollande.

kuma ya marawa jam'iyar shugaba mai ci yanzu Emmanuel Macron baya a zaben shugabancin kasar da ya gabata, bayan da ya sha kaye a zaben fidda gwani na jam'iyyarsa ta 'yan gurguzu a watan Janairu da ya gabata.