Rasha Ta Yi Tir Da Barazana Amurka Kan Gwamnatin Siriya
https://parstoday.ir/ha/news/world-i21694-rasha_ta_yi_tir_da_barazana_amurka_kan_gwamnatin_siriya
Fadar Kremlin ta yi Allah wadai da kakkausar murya kan barazana Amurka ga zargin gwamnatin Siriya da shirin kai hari da sinadari mai guba.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Jun 27, 2017 05:57 UTC
  • Rasha Ta Yi Tir Da Barazana Amurka Kan Gwamnatin Siriya

Fadar Kremlin ta yi Allah wadai da kakkausar murya kan barazana Amurka ga zargin gwamnatin Siriya da shirin kai hari da sinadari mai guba.

kakakin fadar shugaban kasa a Rasha, Dmitri Peskov, ya ce irin wadanan kalamai na barazana marasa tushe da Amurka ke yi, ba abun lamunta ba ne ba ko kadan.

Mista Peskov, ya kara da cewa bai san dalili ba ko kuma hujjojin da ke tursasawa Amurka yin irin wannan zargi ba.

Wata sanarwa dai da fadar White House ta fitar ta yi gargadi ga shugaba Assad akan wani shiri da ta ce yana yi na kai hari da sinadirai masu guba.

Gwamnatin Siriya dai ta jima tana musunta kanta da amfani da makamai masu guba, bayan ta shaidawa duniya cwa ta lalatasu.