Rasha Ta Zargi Amurka Da Kokarin Tayar Da Rikici Akan Iyakokinta
Jul 02, 2017 19:15 UTC
Wani mai nazarin siyasa dan Rasha Alexander Kuznetsov soki girke sojojin kungiyar Nato a gabacin kasashen turai.
Kuznetsov ya ci gaba da cewa girke sojojin kungiyar yarjejeniyar tsaro ta Nato a kusa da iyakokin Rasha, wani shiri ne na Amurka da zummar fada da Rasha.
Har ila yau Kuznetsov ya yi ishara da watsi da alkawalin da Trump ya yi a lokacin yakin neman zabe na kyautata alaka da kasar Rasha, sannan ya kara da cewa; Wannan karya alwalin abinda Rasha ta ke iya fahimta ne saboda kungiyar "Nato' tana da bukatuwa da kirkiro abokin gaba, kuma Rasha ita ce wacce su ka zaba.
Tags