Faransa : Macron Zai Kira Taro Kan canjin Yanayi
https://parstoday.ir/ha/news/world-i22026-faransa_macron_zai_kira_taro_kan_canjin_yanayi
Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron ya sanar a wannan Asabar cewa zai hada wani taro a ranar 12 ga watan Disamba mai zuwa a matsayin na matakin farko kan batun canjin yanayi.
(last modified 2018-08-22T11:30:21+00:00 )
Jul 08, 2017 18:12 UTC
  • Faransa : Macron Zai Kira Taro Kan canjin Yanayi

Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron ya sanar a wannan Asabar cewa zai hada wani taro a ranar 12 ga watan Disamba mai zuwa a matsayin na matakin farko kan batun canjin yanayi.

Wannan dai na zuwa ne shekaru biyu bayan da yarjejeniyar canjin yanayi ta Paris da kasashen duniya suka rattabawa hannu ta fara aiki.

Mista Maccron ya ce bai fidda tsamannin ba zai shawo kan takwaransa na Amurka Donald Trump ba kan ya sake dawowa a cikin wannan yarjejeniyar.

Shugabna Maccron wanda ke bayyana hankan gaban manema labarai a  birnin Hambourg na Jamus a yayin taron G20,  ya ce zai hada wani sabon taro domin daukan sabbin matakai kan canjin yanayi, musamen ta bagaren kudade.

Taron wanda ba'a bayyana inda za'a yin sa ba a kasar ta Faransa zai fi maida hankali kan tattara kudade daga al'umma da kuma ta  bangaran masu zamen kansu kamar yadda akayi alkawari a taron na watan Disamba shekara 2015 data gabata.