UNESCO Ta Sanya Birnin Yazd Cikin Biranen Tarihi Na Duniya
(last modified Sun, 09 Jul 2017 11:12:23 GMT )
Jul 09, 2017 11:12 UTC
  • UNESCO Ta Sanya Birnin Yazd Cikin Biranen Tarihi Na Duniya

A yayin taron ta Karo na 41, Hukumar UNESCO Ta sanya Dadadden garin tahirin nan kasar Iran Yazd a cikin jerin Biranen Tarihi na Duniya

Hukumar gidan telbijin da radio na kasar Iran ta habarta cewa bayan kwashe shekaru 9 da Hukumar UNESCO ta sanya Birnin Yazd cikin jerin Biranan tarihi na Duniya na wucin gadi,a karshen Manbobin Kwamitin sun amince da sanya shi cikin jerin biranan tarihi na Duniya.

Ganin cewa babu ko da mutum daya da ya nuna adawa da sanya birnin Yazd din cikin jerin biranan Tarihi na Duniya, Shugaban Kwamitin ya bukaci mahalarta taron da tabi tare da sanar a hukunce da sanya birnin cikin jerin biranan tarihi na Duniya.

Wannan lamari na zuwa ne a yayin da zaman ya samar da wasu kudurori guda biyu a kan Haramtacciyar kasar Isra'ila, kuma wannan a bangaren Siyasa , babbar nasara ne ga jamhuriyar musulinci ta Iran.