MDD Ta Bukaci Kawo Karshen Duk Wani Rikici A Masallacin Qudus
Majalisar Dinkin Duniya ta jaddada bukatar kawo karshen duk wani rikici tsakanin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila da al'ummar Palasdinu a Masallacin Qudus.
Farhan Haq mataimakin kakakin babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya bukaci al'ummar Palasdinu da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila da su kai zuciya nesa domin sulhunta tsakaninsu da nufin kawo karshen duk wani rikici da tarzoma a Masallacin Qudus.
Farhan Haq ya kuma yi kira da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila da cewa: Dole ne ta dauki matakin canja sabon salon siyasarta kan Palasdinawa a garin Baitu-Mukaddas da kuma Masallacin Qudus domin ganin an samu wanzuwar zaman lafiya da sulhu a Palasdinu.
A gefe guda kuma Fira ministan hukumar cin gashin kan Palasdinawa Rami Hamdullahi ya bukaci kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta O.I.C da ta hanzarta kiran zaman taron gaggawa da nufin daukan kwararan matakai kan bakin zaluncin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila kan al'ummar Palasdinu da Masallacin Qudus mai alfarma.