The Guardian: Trump Ya Kama Hanyar Rusa Kasar Amurka
Jaridar Guardian ta kasar Birtaniya ta watsa wani sharhi a shafinta na yanar gizo da ke cewa, shugaban kasar Amurka Donald Trump ya kama hanyar rusa kasar.
Guardian ta ce bayan shudewar watanni da Trump ya hau kan kujerar shugaban kasar Amurka, ya zuwa yanzu ya rusa shirye-shirye da dama da suke da alaka da ci gaban tattalin arzikin Amurka a bangaren tsare-tsare an ayyukan kudi, kamar yadda haka lamari yake a bangaren kiwon lafiya da kare muhalli.
A bangaren siyasar waje kuma, Guardian ta ce dokar hana yin hijira zuwa Amurka babban kure na siyasa da gwamnatin Trump ta tafka, domin kuwa hakan yana a matsayin nuna kyama ga musulmi ne a hukumance.
Baya ga haka kuma jaridar ta ce hatta kasashen turai da dama ba su gamsu da yadda Trump ke tafiyar da siyasarsa ba, duk da cewa sun sani kan cewa ba shi da masaniya ko wata gogewa a bangaren siyasa, a bin da ya sani kuma yake gabansa kawai shi ne kudi, kuma hakan shi ne babban dalilin da yasa ya kulla kawance da sarakaunan kama karya daga cikin kasashne larabawa, domin ya kwashi daruruwan biliyoyin dalolin man fetur.
Sakamkon jin ra'ayin jama'a na baya-bayan nan da aka gudanr a Amurka ya nuna cewa, kimanin kashi 63% na al'ummar Amurka ba su gamsu da mulkin Trump ba, yayin kashi 37% ne kawai suke mara masa.