Afganistan Ta Yi Maraba Da Shirin Girke Sojojin Amurka
(last modified Tue, 22 Aug 2017 10:57:07 GMT )
Aug 22, 2017 10:57 UTC
  • Afganistan Ta Yi Maraba Da Shirin Girke Sojojin Amurka

Fadar shugaban kasa a Afganistan ta yi maraba da matakin shugaba Donald Trump na girke sojojin Amurka a kasar.

A wata ziyara da ya kai ga wata tawagar sojoji a Kandahar, Shugaban kasar ta Afganistan, Ashraf Ghani ya bayyana cewa, '' wannan rana ce mai cike da tarihi a gare mu, kuma Amurka ta nuna mana cewa tana tare da mu a ko da yaushe''

Mista Trump dai bai bayyana adadin sojin da zai sake turawa kasar ta Afganistan ba, amma jami’an sa sun ce tuni ya amince da a tura karin sojoji 3,900 kan wadanda ke girke a kasar.

A wani labari kuma kungiyar Taliban ta yi fatali da shirin girke dakarun na Amurka, tana mai shan alwashin Afganistan za ta zamanto wata sabuwar makabarta ga Amurkawa, muddun suka ci gaba da kasancewa a kasar.