Alkawarin Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ga Al'ummar Palasdinu
https://parstoday.ir/ha/news/world-i23683-alkawarin_babban_sakataren_majalisar_dinkin_duniya_ga_al'ummar_palasdinu
A ganawarsa da iyalan mutanen da ake tsare da su a gidajen kurkukun haramtacciyar kasar Isra'ila a yammacin ranar Talatar da ta gabata a garin Ramallah na Palasdinu: Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi alkawarin cewa: Majalisar Dinkin Duniya zata dauki matakan kawo karshen irin azaba da tarin matsalolin da al'ummar Palasdinu suke ciki.
(last modified 2018-11-18T09:03:40+00:00 )
Aug 31, 2017 04:54 UTC

A ganawarsa da iyalan mutanen da ake tsare da su a gidajen kurkukun haramtacciyar kasar Isra'ila a yammacin ranar Talatar da ta gabata a garin Ramallah na Palasdinu: Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi alkawarin cewa: Majalisar Dinkin Duniya zata dauki matakan kawo karshen irin azaba da tarin matsalolin da al'ummar Palasdinu suke ciki.

A zaman tattaunawan da ya gudana tsakanin babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterrres da iyalan mutanen da ake tsare da su a gidajen kurkukun gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila: Shugaban kwamitin kula da harkokin Palasdinawa da ake tsare da su a gidajen kurkukun haramtacciyar kasar Isra'ila Isa Qara'qa'a ya gabatar da bukata ga babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres cewa: Akwai bukatar babban zauren Majalisar Dinkin Duniya ya gudanar da zama na musamman kan matsalolin Palasdinawan da ake tsare da a gidajem kurkukun gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila; Yana mai jaddada bukatar cewa: Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniyan ya yi kokarin ganin an saki Palasdinawa fiye da 6,500 da ake tsare da su a gidajen kurkukun haramtacciyar kasar Isra'ila.

A fili yake cewa: Duk wani matakin nuna goyon baya ga Palasdinawan da ake tsare da su a gidajen kurkukun haramtacciyar kasar Isra'ila da bayyana damuwa kan mummunan halin da suke ciki musamman fuskantar matsalolin cin zarafin bil-Adama da babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres zai yi, al'amura ne da za a iya cewa sun zo a makare, duk da cewa matsayin Antonio Guterres kan nuna damuwa dangane da matsalolin Palasdinawa ya fi na Ban Ki Moon tsohon babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya.

Duk da yawan maganganu da kungiyoyin kasa da kasa musamman Majalisar Dinkin Duniya suke yi kan halin tsaka mai wuya da al'ummar Palasdinu suke ciki amma Ban Ki Moon a lokacin da yake rike da mukamin babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya ki ganawa da iyalan Palasdinawan da ake tsare su a gidajen kurkukun haramtacciyar kasar Isra'ila lamarin da ya fuskanci tofin Allah tsine daga sassa daban daban na duniya. 

Yau tsawon shekaru 50 ke nan da al'ummar Palasdinu suke dandana kudarsu a karkashin bakar siyasar zaluncin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila amma har yanzu babu wani takamammen yunkuri da duniya ta yi domin kubutar da su daga wannan mummunan kangi, watakila wannan sabon salo da babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bullo da shi na sauraron matsaloli da ji kai tsaye daga al'ummar Palasdinu ya taimaka a fagen samar da hanyar warware halin tsaka mai wuya da al'ummar Palasdinu suke ciki tsawon shekaru musamman daukan matakin samar da yantacciyar kasar Palasdinu da Qudus zai kasance babban birninta.