Sep 10, 2017 10:53 UTC
  • 'Yan Fafatukar Rohingyas Sun Tsagaita Wuta

Mayakan dake fafatukar kare musulmin 'yan kabilar Rohingya a yankin Arakan na Myammar sun sanar da tsagaita buda wuta har na tsawan wata guda daga wannan Lahadi.

'Yan fafatukar sun dau wannan matakin ne don bada damar isar da kayan agaji ga musulmin na Rohingya da kuma sauren kabilun dake cikin bukata, kamar yadda kungiyar ta (ARSA) ta sanar a shafinta na Twitter. 

wannan dai na zuwa ne bayan da a karon farko gwamnatin Myammar ta sanar da a karon farko kebe matsugunnai ga 'yan kabilar ta Rohingya da ke fuskantar hare-haren jami'an tsaron kasar yau sama da makwanni biyu.

Alkaluman baya bayan nan da MDD ta fitar sun nuna cewa musulmin Rohingya kimanin dubu dari uku ne kawo yanzu suke gudun hijira a kasar Bangaladash.

Tags