Erdogan Yayi Barazanar Kakabawa Yankin Kurdawar Iraki Takunkumi
(last modified Sat, 23 Sep 2017 17:36:21 GMT )
Sep 23, 2017 17:36 UTC

Shugaban kasar Turkiya Recepp Tayyip Erdogan yayi barazanar kakabawa yankin kurdawan kasar Iraki takunkumi saboda shawarar da mahukuntan yankin suka yanke na gudanar da zaben raba gardama na ballewar yankin daga kasar Iraki

A yayin da yake jawabi a zauren MDD ranar juma'a 22 ga watan satumba, Shugaba Recepp Tayyip Erdogan ya sake nanata adawarsa na zaben raba gardama na balllewar yankin kurdawan Iraki daga cikin kasar, sannan ya bukaci a kakkabawa yankin takunkumi a matsayin mayar da martani.

Erdogan ya ce kamata yayi a gaggauta daukar mataki na kakabawa yankin na kurdawan Iraki takunkumi, to sai dai bai yi wani karin haske ba game da irin takunkumin da ya kamata a kakabawa yankin, dagewar mahukuntan  kurdawan kasar Iraki na gudanar da zaben raba gardama na ballewar yankin daga kasar Iraki ya fuskanci martani mai tsanani daga gwamnatin kasar Iraki, kungiyoyin fararen hular kasar tare da kasashen yankin.

A ranar 25 ga watan satumba na wannan shekara da muke ciki ne ake sa ran za a gudanar da zaben raba gardama na ballewar yankin Erbil daga cikin kasar Iraki.

Kafin hakan dai, a ranar 20 ga watan satumba, Ministan harakokin kasashen wajen Turkiya  ya ziyarci yankin na kurdawan kasar Iraki inda ya tattauna da shugabanin yankin tare da bayyana musu damuwar kasar sa na shawarar da suka yanki na  gudanar da zaben raba gardama na ballewar yankin daga cikin kasar Iraki, sannan ya bukaci Shugabanin kurdawan da su tattauna da mahukuntan birnin Bagdaza domin kare kasarsu daga fadawa cikin rikici, akalla abin da mahukuntan birnin Ankara ke jira daga kurdawan kasar Irakin,  watsi da wannan shawarar da suka yanke, tare da kare Kurdawan kasar fadawa cikin rikici  karkashin gwamnatin kasar Iraki.

A nasa bangare, Shugaban kasar Turkiya ya bayyana zaben raba gardamar  a matsayin babban kuskure, sannan ya bukaci al'ummar Turkawa da su yi watsi da wannan mumunar shawara tare da kare kasar Iraki.

A hakikanin gaskiya,fargabar shugaban Erdugan na ballewar kurdawan kasar Iraki, shi ne mumunan sakamakon da zai biyo baya a yankin, domin ballewar yankin kurdawan Iraki zai kasance babbar barazana ga tsaron kasar Turkiya musaman ma a halin da ake ciki, mahukuntan na Turkiya na cikin yaki da kungiyar Turkawan kasar da ake kira PKK, idan yankin kurdawan Irakin ya balle daga kasar Iraki, to mahukuntan birnin Ankara ma na iya rasa yankunan kudu maso gabashin kasar, ganin yadda yankin na kurdawan kasar Iraki ke iyaka da kasar Turkiya.

Dangane da wannan da wannan batu, Ali Bigdaley malamin jami'ar Shahid Behehshti dake birnin Tehran, kuma masanin siyasar gabas ta tsakiya na ganin cewa daya daga cikin damuwar kasar Turkiya na zaben raba gardamar yankin kurdawar kasar Iraki na komawa ne kan yawan kurdawan da kasar Turkiya ke da shi.

A yayin da yake bayani kan goyon bayan da mahukuntan Isra'ila ke nunawa game da wannan zabe, Bigdaley ya ce hakan shi ke nuna cewa yankin zai fuskanci gagarumin sauyi a fagen siyasa, idan kuma aka yi la'akari da irin tarin arzikin man fetur din dake wannan yankin, da kuma matsayinsa a gabas ta tsakiya, Haramtacciyar kasar Isra'ila  na iya zamar da shi wani sansanin ta a yankin, kuma zai kasance babbar barazana ga harakokin tsaron kasashen Iran da Turkiya.