Sep 28, 2017 14:32 UTC
  • MDD : Adadin 'Yan Rohingya A Bangaladash Ya Kai Rabin Milyan

Majalisar Dinikin Duniya ta fitar da wani rahoto dake cewa, adadin 'yan gudun hijira Rohingya dake gujewa kisan kiyashin da ake musu a kasar Myammar ya haura rabin Miliyan.

A rahoton data fitar yau Alhamis, MDD ta ce daga ranar 27 ga watan nan 'yan gudun hijira Rohingya da suka tsallaka iyaka zuwa kasar Bangaladash ya kai 501,800.

Saidai rahoton da kungiyoyin na MDD dake sanya ido kan abunda ke faruwa a yankin sun ce an dan samu raguwar tururuwar 'yan gudun hijira a 'yan kwanakin nan.

MDD dai ta danganta abunda ke faruwa a yankin Rakhine na kasar ta Myammar da yunkurin share wata kabila daga doron kasa da sojojin Myammar da adinin Buda ke yi.

A wannan Alhamis ce aka tsara wata tawagar MDD za ta kai ziyara gadi da ido a yankin, sai dai hukumomin Myammar sun dage ziyara saboda a cewarsu rashin kyawan yanayi.

Tags