Da'esh Ta Dauki Alhakin Kai Hari A Kasar Faransa
https://parstoday.ir/ha/news/world-i24545-da'esh_ta_dauki_alhakin_kai_hari_a_kasar_faransa
Kungiyar 'yan ta'addar ta Da'esh ta sanar da daukar alhakin harin na garin Marseille a jiya lhadi.
(last modified 2018-08-22T11:30:46+00:00 )
Oct 02, 2017 07:14 UTC
  • Da'esh Ta Dauki Alhakin Kai Hari A Kasar Faransa

Kungiyar 'yan ta'addar ta Da'esh ta sanar da daukar alhakin harin na garin Marseille a jiya lhadi.

Kamfanin dillancin labarun  Reuters ya nakalto majiyar A'amaq, da ta saba bijiro da labarun "Da'esh, tana cewa daya daga cikin mayakansu ne ya kai harin.

Mata biyu ne aka kashe ta hanyar sararsu da wukake a tashar jirgin kasa da ke garin Marseille da ke kuduncin kasar ta Faransa.

Sai dai jami'an tsaron kasar Faransa sun kashe maharin ta hanyar harbinsa. "Yan sanda sun ce maharin ya rika yin kabbara.

Da akwai 'yan sanda 200 da aka girke a kusa da tashar jirgin kasan da aka kai harin.

Kasar Faransa tana daga cikin kasashen da 'yan ta'adda suka fi kai wa hare-hare a cikin shekarun bayan nan.