Gargadi Kan Yiyuwar Bullar Kisan Kiyashi A Jamhuriyar Afrika Ta Tsakiya
(last modified Thu, 12 Oct 2017 11:52:04 GMT )
Oct 12, 2017 11:52 UTC
  • Gargadi Kan Yiyuwar Bullar Kisan Kiyashi A Jamhuriyar Afrika Ta Tsakiya

Jami'in Majalisar Dinkin Duniya ya yi gargadi kan yiyuwar bullar kisan kiyashi a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya sakamakon yadda tashe-tashen hankula suke ci gaba da lashe rayukan al'umma a kasar.

A jawabin da ya gabatar a birnin Bangui fadar mulkin Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya a jiya Laraba: Adam Ding mai bada shawara na musamman ga babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya kan hanyoyin kalubalantar matsalar kisan kiyashi a duniya ya bayyana cewa: Akwai bullar alamu da suke nuni da cewa zai yiyu a samu bullar matsalar kisan kiyashi kan jinsin bil-Adama a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya sakamakon yadda matakan tsaro suke ci gaba da tabarbarewa a kasar.

Adam Ding ya kara da cewa: Har yanzu akwai bullar kashe-kashen rayukan bil-Adama a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya a kan tubali na sabanin kabilanci, addini da mahangar siyasa a kasar.