UNESCO : Janyewar Amurka Abun Takaici Ne_Bokova
Babbar Daraktar hukumar kula da ilimi, kimiyya da raya al'adu ta MDD cewa da UNESCO, Irina Bokova, ta ce ta yi bakin ciki sosai da kudurin Amurka na janyewa daga hukumar.
Cikin wata sanarwa da ta fitar game da kudurin na Amurka, Misis Bokova ta ce akwai bukatar inganta aikin samar da ilmi da tattaunawa yayin da ake yaki da tsattsauran ra'ayi, amma abun bakin ciki ne yadda Amurka ta janye daga hukumar a wannan lokaci da ake fuskantar rikice-rikice a wurare daban-daban na duniya.
A jiya ne dai Amurka ta sanar da janyewarta daga hukumar ta (UNESCO) saboda zargin da take yi wa hukumar na nuna kyama ga Isra’ila.
Amurka da UNESCO sun shiga takun tsaka ne tun lokacin da babban taron UNESCO na shekarar 2011 ya zartas da kuduri shigar da Falestinu cikin hukumar a matsayin mamba, al'amarin da ya sanya gwamnatin Amurka sanar da dakatar da biyan kudin da take baiwa hukumar a matsayin mamba don mayar da martani.
Tuni dai Isra'ila ta sanar da daukan mataki irin wannan tana mai cewa ta baiwa ma'aikatar harkokin wajenta damar kimsawa domin ficewa daga hukumar.