Jawabin Trump Ya Maida Amurka Saniyar Ware_ Jonh Kerry
Duniya na ci gaba da yin tur da kalamen shugaban Amurka Donald Trump kan yarjejeniyar nukiliyar kasar Iran wacce ya ki amuncewa da ci gaba da goyan bayan ta tare da shan alwashin kakabawa Iran takunkumi.
Da yake magana kan wannan mataki, da kakkausar lafazi, tsohon sakataren harkokin wajen Amurkar John kerry tur ya yi da matakin , yana mai danganta shi da "ganganci''
Mista Kery ya ce jawabin na Trump ya fi bada karfi kan akida maimakon hujja ko shaida dake bayyane, wanda kuma a cewarsa hakan ya gurgunta karfin Amurka, ya maida ita saniyar ware cikin kawayenta, ya kuma toshe duk wasu hanyoyin warware rikicin da ake yi da Koriya ta Arewa kan shirin nukiliyarta, ya kuma kara tura Amurka zuwa ga shiga yaki.
A ranar Juma'a data gabata ne shugaba Donal Trump ya bayyana manufarsa kan yarjejeniyar nukiliyar da mayan kasashen duniya da suka hada da Amurka suka cimmawa da Iran a 2015 kan takaita shirin nukiliyar Iran.
A jawabin na sa Trump ya ce bai goyanbayan yarjejeniyar da aka shafe shekaru 12 ana kai kawo don ganin an cim mata, tsakanin kasashen da suka hada da Rasha, Sin, Faransa, Amurka, Jamus wacce ta kai ga ya ye ma Iran kalabin wasu jerin takunkuman da aka kakaba mata na tsawan shekaru.