Faransa : Trump Ya Jahilci Yarjejeniyar Nukiliyar Iran_Hollande
(last modified Tue, 17 Oct 2017 05:49:56 GMT )
Oct 17, 2017 05:49 UTC
  • Faransa :  Trump Ya Jahilci Yarjejeniyar Nukiliyar Iran_Hollande

Duniya na ci gaba da yin tur da kalamen shugaba Donald Trump na Amurka kan yarjejeniyar nukiliyar Iran wacce ya ki amuncewa da ci gaba da goyan bayan ta tare da shan alwashin daukan matakin kakabawa Iran din sabbin takunkumi.

Da yake magana kan matakin, tsohon shugaban kasar Faransa, Farancois Hollande, ya ce Trump ya tafka mayan kura kurai biyu kan kin amuncewa da goyan yarjejeniyar da mayan kasashen duniya suka cimma da Iran.

Na farko a cewar Mista Hollande, shugaba Trump ya jahilci yarjejeniyar don bai ma san inda ta nufa ba, kana kuma baida gogewa a sha'anin diflomatsiyya, sannan kuma ya toshe duk wata hanya ta yunkurin da ake na tattunawa da Koriya ta Arewa kan shirin nukiliyar ta.

Tsohon shugaban kasar ta Faransa wanda ke bayyana hakan a birnin Seoul inda yake halartar taron "World Forum Knowledge", wanda kuma a lokacin gwamnatinsa ne aka cimma wannan yarjejeniya, ya bukaci 'yan majalisar Amurka da su juywa matakin na Trump baya domin mutunta yarjejeniyar da mayan kasashen duniya suka cimmawa da Iran a shekara 2015.

Jawabin da Trump ya yi a ranar Juma'a data gabata dai ya maida Amurka saniyar ware tsakanin takwarorinta a cewar masana harkokin siyasa.