Kokarin Kasar Masar Na Bunkasa Alaka Da Kasar Faransa
Ziyarar aikin da shugaban kasar Masar ya kai zuwa kasar Faransa ya fi maida da hankali ne kan bukatar bunkasa alakar da ke tsakanin kasashen biyu a bangarori da dama.
A ganawar da ta gudana tsakanin shugaban kasar Masar Abdul-Fatah Al-Sisi da takwararsa na kasar Faransa Emmanuel Macron a ranar Talatar da ta gabata a birnin Paris, shugabannin kasashen biyu sun jaddada bukatar bunkasa alaka da taimakekkeniya a tsakanin kasashensu musamman a fagen siyasa, tattalin arziki da kuma yaki da ta'addanci. Kamar yadda shugabannin biyu suka tattauna batun matsalar kasashen Siriya da Libiya.
Masharhanta suna bayyana cewa: Ziyarar aikin da shugaban kasar Masar Abdul-Fatah Al-Sisi ya kai zuwa kasar Faransa ta fi maida hankali ne kan bukatar fadada alaka a fagen matakan tsaro da na soji a tsakanin kasashen biyu domin samun nasarar yaki da ta'addanci da suke ci gaba da addabar kasashen biyu da kuma bunkasa harkar tattalin arziki musamman batun zuba hannun jari a kasar Masar.
Hakika matsalar habakar ayyukan ta'addanci a yankin arewacin Afrika yana daga cikin manyan matsaloli da suke addabar kasashen yankin da ma kasashen yammacin Turai musamman kasar Faransa, inda a halin yanzu kungiyar ta'addanci ta Da'ish ta kama wasu yankunan kasar Libiya da suke makobtaka da kasar Masar, kuma 'yan ta'addan kasa da kasa da aka jibge a kasashen Siriya da Iraki suka fara komawa kasashensu ciki har da kasashen yammacin Turai bayan kashin da suka sha a kasashen na Iraki da Siriya.
Batun bunkasa harkar tattalin arziki tsakanin Masar da Faransa yana daga cikin muhimman batutuwan da suka kai shugaba Abdul-Fatah Al-Sisi zuwa kasar Faransa saboda rahotonni suna nuni da cewa: Mafi yawan al'ummar Masar suna fama da matsalar tattalin arziki lamarin da ke kara zaburar da su kan nuna adawa ga gwamnatin Al-Sisi, sakamakon haka shugaban kasar ta Masar yake kokarin ganin ya kullar kyakkyawar alakar tattalin arziki da kasar Faransa da nufin janyo kamfanonin kasar zuwa Masar da nufin zuba hannun jari. Sai dai hanzari ba gudu ba, wannan kokari na shugaban kasar Masar zai iya fuskantar matsaloli musamman daga kungiyoyin kare hakkin bil-Adama da a kullum suke jan hankalin kasashen yammacin Turai musamman Faransa kan sanya batun kare hakkin bil-Adama a Masar ya zame jagoranta na kyautata duk wata alaka da gwamnatin kasar.