Sojojin Siriya Sun Fatattakin Jiragen Yakin 'Isra'ila' Da Suka Shigo Kasar
Sojojin Siriya sun harba alal akalla makamai masu linzami guda hudu kan wasu jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra'ila a lokacin da suke kokarin kai wasu hare-hare a wasu wajaje a kusa da birnin Damaskus, babban birnin kasar Siriyan.
Kamfanin dillancin labaran Al-Masdar ya jiyo wasu majiyoyin sojin kasar Siriyan suna fadin cewa sojojin Siriyan sun kai hari da wasu makamai masu linzami masu kakkabo jiragen yaki kan wasu jiragen yakin Haramtacciyar kasar Isra'ila da suka so kai hare-haren wuce gona da iri cikin kasar Siriyan a yau din nan Asabar.
Majiyar ta kara da cewa jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra'ilan sun harba wasu makamai masu linzami kan wani sansanin sojin kasar Siriyan ne da ke wajen garin na Damaskus, sai dai kuma na'urorin kariya na sojojin Siriyan sun sami nasarar kakkabo makamai masu linzamin kafin ma su fado kasa.
Wannan dai ba shi karon farko da jiragen yakin HKI suke kai hari kasar Siriyan ba, lamarin da ya sanya sojojin Siriyan barazanar mayar da martani matukar dai HKI ta ci gaba da kai irin wadannan hare-haren.