Amurka Da Saudiyya Sun Taimakawa (IS) Mallakar Muggan Makamai_ Rahoton (CAR)
Kungiyar (CAR) dake sa ido kan yadda ake amfani da makaman yaki da kayan soji na kasa da kasa, ta fitar da wani rahoto, wanda ke cewa makaman yakin da kasashen Amurka da Saudiyya suka mikawa 'yan tawaye a Siriya ya taimakawa 'yan ta'adda IS sosai.
A cikin rahoton da ta fitar, kungiyar ta Conflict Armament Research (CAR) dake da cibiya a Birtaniya, ta ce na bincike na tsawan shekaru uku data gudanar kan makamai iri daban daban har 40,000 da 'yan ta'addan IS sukayi amfani dasu, ya nuna cewa makamai ne da kasashen Saudiyya da Amurka suka mikawa 'yan tawayen Siriya.
Hakan dai a cewar rahoton ya taimakawa kungiyar 'yan ta'adda ta IS mallakar muggan makamai masu yawa.
Rahoton ya ce Amurka ba tada 'yancin mikawa 'yan tawayen makaman ciki harda wadandan ta samu daga wasu kasashen Turai, wanda bai zo da mamaki ba kasancewar ba shi ne karon farko ba, don kuwa kasashen Amurka da Faransa da Kuma Birtaniya sun taimakawa 'yan tawayen Siriya da makamai, wanda kuma a cikin lokaci kadan suka fada hannun kungiyar Al'Nosra dake da alaka da kungiyar Al-Qaïda.
Ko baya ga shi a cewar rahoton horon da hukumar leken asirin Amurka ta CIA ta baiwa 'yan tawayen Siriya a Jodan ya taimakawa 'yan ta'adda IS sosai da makamai kasancewar dayewa daga cikinsu sun tsere da makaman da kayan aiki suga shiga kungiyar IS, lamarin da ma ya cilastawa AMurkar dakatar da baiwa 'yan tawayen horo.