Fafaroma Francis ya ja hankali kan ‘yan gudun hijira
Shugaban cocin katolika, Fafaroma Francis ya bukaci mabiyansa da kar su manta da halin da 'Yan gudun hijira ke ciki wadanda tashin hankali ya tilastawa barin kasashen su a lokacin bukukuwan Kirsimeti.
A jawabin da ya gabatar a jajibirin bikin Kirsimeti a daren jiya Lahadi a cocin Saint Peter's da ke fadar Vatican, shugaban ya kwatanta lamarin da labarin Maryam a lokacin da take nakudar haihuwar Annabi Isa (AS).
Fafaroma Francis ya ce akwai darasi kan labarin Yusuf da Maryamu, mun ga yadda aka tilastawa iyalai watsewa mun ga yadda aka tilastawa wasu miliyoyin mutane tserewa daga muhallan su.
Fafaroman ya ce duniya ta ga yadda aka tilastawa miliyoyin mutane barin gidajen su da kuma kasashen su, yayin da ya zargi wasu shugabanni da haifar da matsalar domin biyan bukatun kan su.