Paparoma Ya Sake Yin Watsi Da Matsayar Trump Kan Birnin Kudus
Shugaban mabiya darikar Katolika na duniya Paparoma Francis ya sake jaddada matsayar fadar Vatican din na kin amincewa da matsayar da shugaban Amurka Donald Trump ya dauka kan birnin Kudus yana mai bayyana kafa kasashe biyu, wato Palastinu da Isra'ila a matsayin hanyar magance rikicin matsalar Palastinu.
Paparoma Francis din ya bayyana hakan ne a lokacin da yake isar da sakon Kirsimeti da miliyoyin mabiya addinin Kirista a duk fadin duniya a yau din nan Litinin inda yayi kiran da a yi addu'oi don samar da yanayin da za a koma kan teburin tattaunawa tsakanin Palastinawa da Isra'ilawa da nufin cimma yarjejeniyar sulhu da zai tabbatar da kasashe biyu masu kan iyakokin da kasashen duniya suka amince da su.
Wannan dai shi ne karo na biyu da Paparoman yayi magana kan birnin Kudus tun bayan da shugaban Amurka, Donald Trump, ya sanar da matsayar gwamnatinsa na amincewa da Kudus din a matsayin babban birnin haramtacciyar kasar Isra'ila lamarin da yake ci gaba da fuskantar tofin Allah tsine daga kasashe daban-daban na duniya.
Jawabin na Paparoma ya zo ne 'yan kwanaki bayan da kimanin kasashe 128 na duniya suka amince da wani kuduri na babban zauren MDD da ya bukaci Amurkan ta janye wannan matsaya na ta kan birnin na Kudus.
A yau ne dai miliyoyin Kiristoci a duniya suke ci gaba da gudanar da bukukuwan Kirsimeti don tunawa da ranar da aka haifi Annabi Isa al-Masihu (a.s).