Shugaban Kasar Bolivia Ya Soki Matsayar Gwamnatin Guetamala Kan Birnin Kudus
Shugaban kasar Bolivia Evo Morales yayi kakkausar suka ga matsayar da gwamnatin kasar Guetamala ta dauka na mayar da ofishin jakadancinta a haramtacciyar kasar Isra'ila daga birnin Tel Aviv zuwa birnin Kudus.
Jaridar Lavanguardia ta kasar Spain ta jiyo shugaban kasar Bolivian Evo Morales yana fadin cewa wannan matsaya da gwamnatin Guetamalan ta dauki yana a matsayin sayar da mutumci da daukakar kasar ne ga Amurka don samun wani abin da bai taka kara ya karya ba.
A ranar Asabar din da ta gabata ce shugaban kasar Guetamalan Jimmy Morales, bayan wata tattaunawa da yayi da firayi ministan haramtacciyar kasar Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya sanar da cewa zai dage ofishin jakadancin kasar a "Isra'ilan" daga Tel Aviv zuwa birnin Kudus.
Kasar Guetamala dai tana daga cikin kasashe 9 da suka kada kuri'ar kin amincewa da wani kuduri da aka gabatar a babban zauren Majalisar Dinkin Duniya da ya bukaci Amurka ta janye daga matsayar da ta dauka na sanar da birnin Kudus din a matsayin babban birnin haramtacciyar kasar Isra'ilan duk kuwa da amincewa da kudurin da wasu kasashe 128 na duniya suka yi.