An tsaurara matakan tsaro a kan iyakokin Faransa da Balgium
Kasashen Faransa da Belgium sun karfafa matakan tsaro a kan iyakokin kasashen su saboda barazanar harin 'yan ta'adda
Bayan da aka cabke daya daga cikin dan ta'addar da ake zarkin shi da kai harin watan Nuwambar shekarar da ta gabata na birnin Paris a kasar Balguim kasashen sun karfafa matakan tsaro a kan iyakokin su saboda fargabar sake kai wani hari na ta'addanci.
'Yan sandar kasar Belguim ne suka kame Salah Abdelsalam babban mutumin da ake zargi da kai hare-hare a wurare daban daban a birnin Paris na kasar Faransa a Nuwambar bara inda mutane sama da 130 suka rasa rayukansu, baya ga wasu da dama da suka jikatta sakamakon jerin hare-haren.
Gwamnatin kasar Faransa ta bayyana cewa a kwai yiyuwar shigar 'yan ta'adda cikin kasar domin haka za ta tura yawan dakarunta domin taimakawa jami'an 'yan sanda dubu biyar dake kan iyakar kasar da Belgium.
Gwamnatin kasar Belguin ta gabatar da tuhuma a hukumance kan Salah Abdelsalam , Sai dai Lauyansa ya ce zai kalubalanci yunkurin mekasa ga magabatan kasar Faransa.