Kasar India Ta Soke Yarjejeniyan Sayan Makamai Daga Haramtacciyar Kasar Isra'ila.
(last modified Sat, 06 Jan 2018 06:39:51 GMT )
Jan 06, 2018 06:39 UTC
  • Kasar India Ta Soke Yarjejeniyan Sayan Makamai Daga Haramtacciyar Kasar Isra'ila.

Gwamnatin kasar India ta bada sanarwan soke kwangilar sayan makamai wadanda kimar su ya kai dalar Amurka miliyan 500.

Gwamnatin kasra India ta dau wannan matakin ne a dai-dai lokacin da Priministan Haramtacciyar kasar Isarila yake shirin kai ziyarar aiki a kasra ta India

A tsakiyar watan Janairun da muke ciki ne ake sa ran Priministan Haramtacciyar kasar Israila zai kai ziyarar aiki a kasar ta india.

Kamfanin kera makamai na haramtacciyar kasar Usarila {Raphael } ya bayyana cewa soke yarjejeniyar sayan makaman ya zo ta bangare guda, wato bangaren gwamnatin kasar India. Kamfanin ya kuma kara da cewa makaman da ya kamata gwamnatin kasar India ta saya daga kamfanin su ne Garkuwan tankunan yaki wadanda ake kira  "Spike" 

Kasar India dai tana daga cikin manyan kasashen duniya da suke sayan makamai daga haramtacciyar kasar Israila, kuma ta bayyana dalilin soke wannan kwantaragi kan cewa tana son karfafa masana'antar makamanta na cikin gida ne. 

Ministan tsaron kasar India a lokacin da yake karin bayani kan wannan mataki na soke sayan makamai daga Haramtacciyar kasar Isaraila ya ce a halin yanzu kasar India tana samar da kashi 40% kacal na makaman da take bukata, sauran kuma tana sayansu ne daga kasashen duniya.

Ministan ya kara da cewa dogaron da kasar ta yi na shigo da mafi yawan makaman da take bukata daga kasashen waje babbar barazana ce , kuma hatsari ne babba, don haka a halin yanzu ta kuduri aniyar samar da mafi yawan makaman da take bukata daga cikin gida.

Har'ila yau  Priministan kasar ta India "Narandra Modi" ya bayyana cewa gwamnatinsa ta samar da wani shiri mai suna "Made In India" wato an kera shi a India, wanda a karkashin wannan shirin yana son kasar India ta shiga cikin jerin kasashe masu sayar da makamai ga kasashen waje ne. Don haka a halin yanzu kasar zata tallafa wa kamfanonin cikin gida don ganin sun fadada ilmi da aikin samar da irin wadannan abubuwan bukata tare da dogaro da abin da suke da shi a cikin gida. 

Sai dai a wani bangaren kuma wannan matakin da kasar india ta dauka yana iya zama barzana ga kasashe kamar Pakisatan da kuma China wadanda suke gasa da ita a wannan bangaren