Bayanin Jagora a Hubbarin Imam Ridha (a.s)
(last modified Sun, 20 Mar 2016 16:47:06 GMT )
Mar 20, 2016 16:47 UTC
  • Bayanin Jagora a Hubbarin Imam Ridha (a.s)

Jagoran juyin juya halin musulinci Ayatullahi Ali Khamna'i ya gabatar da jawabi a gaban milyoyin maziyartan hubbarin Imam Ridha (a.s) dake birnin Mashhad.

Yayin gudanar da jawabin a marecen yau, jagora ya bayyana cewa Jumhoriyar musulinci ta Iran ba za ta yi sassauci ba kan matsayinta da kuma tunkarar kasashe masu girmar kai a duniya irinsu Amurka.

Jagora ya ce Amurka na son Jumhoriyar musulinci ta iran ta kauda kai ga wadanda da ake zalinta a yankin kamar Al'ummar Palastinu, Yemen, da kuma Bahren ta kuma daina goyon bayansu a siyasance.

Ayatullahi Ali khemna'i ya tabbatar da cewa matsalar kasashen Siriya, Iraki da Palastinu wata damuwa dake cikin idanuwan Al'ummar Iran domin haka babu yadda za a yi wannan damuwa ta kushe matukar ba sun samu cikekken 'yanci ba.

Yayin da ya koma kan yarjejjeniyar nukiliyarta na zaman Lafiya da ta cimmawa tare da manyan kasashen duniya, jagora ya bayyana cewa a rubuce an cimma yarjejjeniya amma a aikace batun ba haka yake ba, domin magabatan Amurka ba su yi aiki da wannan yarjejjeniya ba saboda sun ci gaba da kakabawa kasar ta Iran takunkumi.

Yayin da yake ishara kan wasu kasashen yankin da suke dasawa da gwamnatin Haramcecciyar kasar Isra'ila, jagora ya ce wadannan kasashe na son jumhoriyar musulnci ta Iran ta sasanta da Haramcecciyar kasar Isra'ila da kuma hakan ba zai samu ba.