Martanin Masar ga Ma'aikatar harakokin wajen Amurka
Ministan Harakokin wajen kasar Masar ya mayar da martani kan sukan da Magabatan Washinton suka yi wa kasar dangane da batun take hakin bil-adama
Yayi da yake watsi kan zarkin da magabatan washinton ke yiwa kasar sa na take hakin bil-adama a yau, Samih Shukri Ministan harakokin wajen Masar ya ce wannan zarke zarke da ma'aikatar harakokin wajen Amurke da wasu kasashen yamma ke yiwa Masar ba zai wani tasiri ba ga magabatan Alkahira kuma wannan ba zai hana su ci gaba da aiyukan ci gaban kasar da suke yi.
Magabatan Washinton sun bukaci da a gudanar da bincike kan Gwamnatin ta Masar, musaman ma bayan da kungiyoyin farar hula na kasar suka bukaci taimakon kasashen waje kan yadda ake take hakin bil-adama musaman ma masu adawa da Gwamnatin kasar.
'Yan adawa na ganin cewa yaki da ta'addanci da Gwamnatin ta Masar ke yi ya rikita zauwa rusa 'yan adawa kuma rashin Majalisar dokoki na daga cikin musabbabin karuwar karya dokoki da Gwamnatin Alsise ke yi wajen ci gaba da ganin bayan 'yan adawa.