Hatsarin Jirgin Sama Ya hallaka Sojoji Biyar A Faransa
Akalla Sojoji 5 ne suka rasa rayukansu sanadiyar hatsarin jiragen sama na sojan Faransa guda biyu.
Hukumar gidan talabijin da radio na kasar Iran ya habarta cewa a wannan juma'a ce wasu jiragen saman soja da ake kira da helikofta na kasar Faransa biyu suka hadu da juna a kudancin kasar, hatsarin da ya yi sanadiyar mutuwar sojoji biyar.
Rahoton ya ce jiragen na makarantar koyar da tukn jiragen sama ne na Dakarun kasar na kasa.ya zuwa yanzu dai ba a bayyana sandin da ya janyo hatsarin jiragen biyu ba.
A bangare guda, rikici ya barke a tsakanin 'yan Afganistan da 'yan Afrika a sansanin tsugunar da 'yan gudun hijira na Calais da ke kasar ta Faransa.
A halin yanzu mutane 22 ne ke kwance asibiti ciki kuwa har da wasu 'yan kasar Iritiriya 4 masu shekaru tsakanin 16 zuwa 18, fadan dai ya samo asali ne ya yin layin karbar abinci lokacin da wa ni dan gudun hijira da ga Afganistan ya fara harbe harbe da bindiga.
Wani jami'i a sansanin ya shaidawa manema labarai cewar sansanin na Calais dai yayi zaman matsugunin sama da mutane dubu 10 masu aniyar tsallakawa Turai an kuma rushe shi tun a shekara ta 2016.
Sai dai har yanzu daruruwan 'yan gudun hijira sun yi kama guri zauna tare da kudurin shiga Turan ta barauniyar hanya. Jami'an tsaro sun kwatanta munin al'amarin da irinsa na farko da ya faru tun a lokacin da aka kirkiri sansanin a shekara ta 2015.