Firayi Ministan India Zai Ziyarci Yankunan Palasdinawa
(last modified Mon, 05 Feb 2018 17:14:25 GMT )
Feb 05, 2018 17:14 UTC
  • Firayi Ministan India Zai Ziyarci Yankunan Palasdinawa

Firayi Ministan India, Narendra Modi, zai kai wata zoyara a yankunan Palasdinawa a wani ran gadi da zai kaddamar a yankin gabas ta tsakiya.

Wannan ziyarar na zuwa ne makwanni kadan bayan ganawarsa da firayi ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu a birnin New Delhi.

Ana dai kallon wannan ziyara a matsayin nuna goyan bayan India ga al'ummar Palasdinu akan mamayar da yahudawan sahayoniya ke mata duk da kusancinta da Isra'ilar.

A ranakun 9 zuwa 12 ga watan nan ne, Mista Modi, zai fara ziyara a yankin na gabas ta tsakiya inda zai ziyarci kasashen Oman da hadadiyyar daular Larabawa, kuma ita ce ziyararsa ta farko a yankunan Palasdinawa.

India dai na cikin kasashen da suka yi fatali da matakin Amurka na ayyana Qudus a matsayin babban birnin mahukuntan yahudawa 'yan nanaya na Isra'ila.