Damuwar MDD Kan Halin Da Al'umma Gaza Ke Ciki
Saktare Janar Na MDD ya bayyana damuwarsa kan halin da al'ummar zirin Gaza ke ciki, tare da daukan alkawarin ci gaba da kokari na magance matsalar kafa gwamnati biyu domin kawo karshen rikici tsakanin Haramtacciyar kasar Isra'ila da Palastinu.
Kamfanin dillancin labaran Xin huwa daga hedkwatar MDD ya nakalto António Guterres sakatare janar na MDD a jiya Litinin yayin wani zama na kwamitin kare hakkin al'ummar Palastinu ya ce matukar dai aka samu tsaiko wajen isar da kayan agaji ga mazauna yankin zirin Gaza, to nan gaba yankin zai fada cikin mawuyacin hali.
Jami'an MDD sun hango cewa matukar dai ba a dauki matakan da suka dace ba wajen farfado da yanayin yankin da kuma tabbatar da bukatar al'ummar yankin da kuma sake gine-ginen da HKI ta rusa zuwa shekarar 2020, to nan gaba rawuya a yankin za ta yi wuya.
A yayin da yake ishara kan raguwar kasafin kudin Majalisar, saktare janar na MDD ya bayyana cewa yana cikin matukar damuwarsa saboda kasawar Majalisar wajen daukar nauyin karatun yara da kuma kiyon lafiya na 'yan gudun hijrar Palastinu.