Faransa Ta Bayyana Damuwarta Kan Halin Da Al'ummar Siriya Ke Ciki.
(last modified Thu, 08 Feb 2018 17:55:21 GMT )
Feb 08, 2018 17:55 UTC
  • Faransa Ta Bayyana Damuwarta Kan Halin Da Al'ummar Siriya Ke Ciki.

Wakilin Kasar Faransa a MDD ya bayyana damuwarsa kan halin da fararen hula ke ciki a kasar Siriya

Kamfanin dillancin labaran Irna ya nakalto Francois Delatre wakilin kasar Faransa a MDD har ila yau ya bukaci tsagaita wuta da fadin kasar ta Siriya,inda ya ce yanayin da kasar siriya ta tsinki kanta ciki a cikin 'yan shekarun nan shi ne mafi muni a cikin tarihin kasar, kuma daga shekarar da ta gabata zuwa yanzu yanayin ya kara munana.

Jami'in na kasar Faransa ya tabbatar da bukatar hadin kai na al'ummar kasar baki daya domin sake gina kasar siriya, inda ya sake meka bukatarsa ga kwamitin tsaron MDD na kokarin magance matsalar tsaro da siyasa da kasar ke fama da su.

Kimanin shekaru bakwai kenan, da kasar ta Siriya ta fada cikin yaki bayan da wasu kasashen yamma suka kwaso 'yan ta'adda daga kasashen duniya daban-daban suka kuma basu makamai domin kifar da halastaciyar gwamnatin siiya.

Kungiyoyi irin su ISIS, da Jabhatu-nusra na daga cikin kungiyoyin da kasashen yamma gami da Amurka suka kafa tare da taimaka musu da makamai, horo, kudi tare kuma da basu kariya a kasar ta siriya.

To saidai a halin da ake ciki, nasarar da Dakarun tsaron siriya da kuma kungiyoyin gwagwarmaya ke samu kan 'yan ta'addar na ci gaba da bakantawa magoya bayansu rai.