Shugabar Kasar Mauritius Za Ta Yi Murabus Saboda Badakalar Cin Kudade
Shugabar kasar Mauritius Ameenah Gurib-Fakim ta sanar da cewa za ta yi murabus daga mukaminta a mako mai zuwa bayan da aka zarge ta da amfani da katin bashi na sayen kayayyaki da wata kungiya ta kasa da kasa ta ba wa gwamnatin kasar wajen sayen kayayyakin sawa da kuma gwala gwalai wa kanta.
Firayi ministan kasar Mauritius din Pravind Jugnauth, ne ya shaida wa manema labarai hakan a jiya Juma'a inda ya ce shugaba Gurib-Fakim za ta yi murabus a ranar 12 ga watan Maris din bayan bikin shekaru 50 da kafa kasar, yana mai cewa shugabar kasar ce ta shaida masa hakan.
A jiya ne dai firayi ministan ya jagoranci wani taro na manyan jami'an kasar inda suka amince da fara gudanar da tsare-tsaren da suka kamata na tsige shugabar kasar sakamakon kin amincewa ta yi murabus din bisa wannan zargi da ake mata.
Shugaba Gurib-Fakim, wacce ita ce shugabar kasar mace ta farko ta musanta cewa ta aikata wani abin da bai dace tana mai cewa tuni ta mayar da kudin da ake magana kansu.
Kafafen watsa labarai dai sun ce shugabar kasar ta yi amfani da katin ne wanda cibiyar Planet Earth Institute da take ba da tallafi a bangaren ilimi ta bayar wajen sayen kayayyaki a Italiya da Dubai.