Amurka : Hadari Ne Tattaunawa Da Koriya Ta Arewa_ Hillary Clinton
(last modified Sun, 11 Mar 2018 05:51:29 GMT )
Mar 11, 2018 05:51 UTC
  • Amurka : Hadari Ne Tattaunawa Da Koriya Ta Arewa_ Hillary Clinton

Tsohuwar jami'ar diflomatsiyar Amurka, Hillary Cliton, ta ce hadari diflomatsiyya ne tattaunawar da shugaban kasar Donald Trump ke shirin yi da gwamnatin Koriya ta Arewa.

Misis Clinton 'yar takara jam'iiyar demokrate data sha kaye a zaben da ya gabata, ta ce '' idan har gwamnatin Trump na son yin wannan tattaunawa da koriya ta Arewa da kuma makamman nukiliyarta, to ya zamana  ta yi tanadin kwararun jami'an diflomatsiya, wanda babu su a wannan gwamnatin ta Trump.

Clinton ta ce zuwan gwamnmatin Trump, ya sa Amurka ta rasa kwararun jami'an diflomatsiya.

Wannan dai na zuwa ne bayan da shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-un ya ce a shirye ya ke ya gana da takwaransa na Amurka Donald Trump nan zuwa watan mayun wannan shekara, tare da yin alkwarin cewa, zai dakatar da gwaje-gwajen makaman nukiliya da kasar ke yi.

Wannan dai, tabbaci ne da ke kunshe a wani sako da shugaban na Koriya ta Arewa ya aika wa takwaransa na Amurka ta hannun wasu manyan jami’an gwamnatin Koriya ta Kudu, kuma tuni shugaban na Amurka Donald Trump ya amince yin ganawa da takwaransa nasa Kim Jong-un.