Shugaban Amurka Ya Kori Saktaren Harakokin Wajen Rex Tillerson
(last modified Tue, 13 Mar 2018 19:03:28 GMT )
Mar 13, 2018 19:03 UTC
  • Shugaban Amurka Ya Kori Saktaren Harakokin Wajen Rex Tillerson

Shugaban Amurka Donald Trump ya kori sakataren harkokin wajen kasar Rex Tillerson daga mukaminsa.

 A wani sakon ba-zata da ya wallafa a shafinsa na Twitter, shugaban na Amurka ya ce ya maye gurbin Mr Tillerson din ne da shugaban hukumar tattara bayanan sirrin kasar CIA, Mike Pompeo. sannan an bayyana Gina Haspel a matsayin wacce za ta maye guebin Mr Pompeo a hukmar ta CIA, mace ta farko da za ta jagoranci hukumar.

Rahotanni sun ce akwai rashin jituwa tsakanin ShugabaTrump da tsohon saktaren harakokin wajen kasar Rex Tillerson, musamman ma  kan manufofin harkokin wajen kasar - kama daga batun yarjejjeniyar da kasar Iran ta cimma da manyan akasashen Duniya kan shirin nukiliyarta na zaman lafiya da  kuma batun Korea ta Arewa .

A jiya  Litinin ne tsohon sakataren harkokin wajen na Amurka ya kai ziyara Najeriya kuma lokacin da ya gana da Shugaba Muhammadu Buhari, ya jaddada aniyar kasarsa wurin taimakwa Najeriya kan yaki da ta'addanci.