Jami'an Tsaro Sun Kame Tsohon Shugaban Kasar Faransa
(last modified Tue, 20 Mar 2018 12:09:09 GMT )
Mar 20, 2018 12:09 UTC
  • Jami'an Tsaro Sun Kame Tsohon Shugaban Kasar Faransa

An kama Nicholas Sarkozy ne bisa zarginsa da ake yi da cin hancin da rashawa a lokacin zaben shugaban kasa na 2007.

Jaridar Lo Monde ta kasar Faransa ta ce kamun da aka yi wa Sarkozy ya shafi zarginsa da ake yi da karbar kudade daga marigayin shugaban kasar Libya Mu'ammar Khaddafi, kuma a yanzu ana ci gaba da yi masa tambayoyi.

Kudaden da ake zargin Khaddafi ya bai wa Sarkozy domin ya yi yakin neman zabe, sun kai Euro miliyan 50. Bugu da kari ana zargin Sarkozin da yin amfani da mukaminsa na shugaban kasa domin cimma wasu manufofinsa na kashin kansa.

Tun a 2012 ne aka bude bincike akan laifukan da ake tuhumar Sarkozi da su, sai dai kuma an sami tsaiko na ci gaba da binciken.