Kotun 'Isra'ila' Ta Daure, Ahed Tamimi, Watanni 8 A Gidan Yari
https://parstoday.ir/ha/news/world-i29292-kotun_'isra'ila'_ta_daure_ahed_tamimi_watanni_8_a_gidan_yari
Wata kotun haramtacciyar kasar Isra'ila ta yanke hukumcin daurin watanni 8 a gidan yari wa Ahed Tamimi, budurwar nan Bapalastiniya wacce aka dauki hotonta tana mari da kuma bugu wani sojan 'Isra'ilan' a Yammacin Kogin Jordan.
(last modified 2018-08-22T11:31:35+00:00 )
Mar 22, 2018 05:19 UTC
  • Kotun 'Isra'ila' Ta Daure, Ahed Tamimi, Watanni 8 A Gidan Yari

Wata kotun haramtacciyar kasar Isra'ila ta yanke hukumcin daurin watanni 8 a gidan yari wa Ahed Tamimi, budurwar nan Bapalastiniya wacce aka dauki hotonta tana mari da kuma bugu wani sojan 'Isra'ilan' a Yammacin Kogin Jordan.

Kafafen watsa labarai sun jiyo lauyan Ahed Tamimin, Gaby Lasky yana fadin cewa a jiya Laraba ce kotun ta yanke wa Ahed Tamimin 'yar shekaru 17 a duniya daurin watanni 8, budu da kari kan tarar dala 1,400.

Ahed Tamimi, wacce aka kawo ta kotun a daure cikin ankwa, ta yi watsi da hukuncin tana cewa mai shaida wa 'yan jaridar da suka taru a kotun da ke gidan yarin Ofer na soji da ke kusa da garin Ramallah cewa ba za a taba samun adalci karkashin mamaya ba.

A watan Disambar bara ne dai sojojin  'Isra'ilan' suka kama Ahed Tamimi da mahaifiyarta, Nariman, bayan fitar da wasu faifan bidiyon da ke nuni da Ahed din tana marin wani sojan Isra'ilan da suka shigo yankunansu.