Amurka Ta Dage Haraji Kan Karafa Ga Abokan Huldarta
Shugaba Donald Trump na Amurka ya bada umurnin dage haraji kan karafa da dalma ga kasashen da ya kira abokan huldar kasarsa masu mahimmanci ciki har da tarayya turai.
Dage harajin kan shigo da karafen da dalma daga kasashen an dage shi har zuwa ranar 1 ga watan Mayu na wannan shekara, a cewar wata sanarwa daga fadar White House.
Matakin dai ya shafi har da wasu kasashe mambobin kungiyar tarayya turai ta (EU) da suka hada da Argantina, Austra, sai Brazil, Canada, Mexoco da kuma Koriya ta Kudu.
Trump ya ce ko wanne daga cikin wandannan kasashen na taka mahimmiyar rawa kan sha'anin tsaro da Amurka
A farkon watan Maris din nan ne Donald Trump ya sanya hannu ga dokar haraji kan karafa da dalma da ake shigo dasu Amurkar, lamarin da ya tayar da kace nace ba kadan ba tsakanin Amurkar da abokan huldarta musamman na Turai wandanda suka ce zasu mayar da martani