Faransa : Za'a Gurfanar Da Sarkozy Gaban Kotu
Tsohon shugaban kasar Faransa, Nicolas Sarkozy, zai gurfana gaban kotu ladabtarwa kan zargin cin hanci da rashawa da kuma yunkurin hana alkali gudanar da aikinsa.
Kotun dai zata maida hankali ne kan wasu hirarrakin wayar tarho da aka nada a shekara 2014, wandanda a ciki ake zargin Mista Sarkozy da neman shawo kan alkalin dake bin diddigin batun ta hanyar yi masa tayin cin hanci.
Ana sa ran alkali Gilbert Azibert da kuma lauyen Sarkozy zasu bayyana gaban kotun, koda yake labarin na cewa Sarkozy zai kalubalanci gurfanar da shi gaban kotun.
Ko baya ga hakan ana zargin Sarkozy a wata badakala ta karbar kudi daga tsohon shugaban kasar Libiya Mu'ammar Ghaddafi, don yin gudanar da yakin neman zabensa a cikin shekara 2007.
Wannan mataki dai ba karamar koma baya bane ga Sarkozy wanda yayi kokarin sake dawowa mulki a watan Nuwamban shekarar 2016 amma bai samu nasara ba.