Faransa Ta Kori Wasu Mutane 20 Daga Cikin Kasar
(last modified Sat, 31 Mar 2018 19:09:23 GMT )
Mar 31, 2018 19:09 UTC
  • Faransa Ta Kori Wasu Mutane 20 Daga Cikin Kasar

Ma'aikatar cikin gidan Faransa ta sanar da korar mutane 20 da ta zarge su da tsattsauran ra'ayi cikin shekarar 2017

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya nakalto Gérard Collomb ministan cikin gidan kasar a wannan asabar na cewa a cikin shekarar 2017 din da ta gabata, gwamnati ta tisa geyar masu tsattsauran ra'ayi 20 zuwa kasashensu, domin kai irin wadannan mutane gidajen kurkuku nada hatsarin gaske.

To saidai ministan bai sanar da ko 'yan wasu kasashe ne aka kora ba.

Wannan sanarwa ta ministan cikin gidan kasar Faransan na zuwa ne a yayin da gwamnati ke shan suka na kasawa wajen daukan kwararen matakan tsaro a kasar.

A bangare guda, 'yan adawar kasar ta Faransa sun bukaci gwamnati da ta dauki kwararen matakan tsaro da kuma mataki mai tsanani ga mutanan da aka sanya cikin jarin masu tsattsauran ra'ayi a ciki kasar da ma duniya gaba daya.