Amurka Ta Kakaba Wa Wasu Jami'an Rasha 38 Takunkumi
Ma'aikatar baitalmalin Amurka, ta sanar da kakaba wa wasu jami'an Rasha su 38 takunkumi, ciki har da wasu makusanta shugaban Rashar Vladimir Putin.
Sakataren harkokin kudi na Amurkar, Steve Mnuchin, ya sanar da cewa an dau wannan matakin ne kamar yadda dokar kasar ta tanada kan duk wasu abokan gaban Amurka.
Daga cikin manyan jami'an Rasha da sabon takunkumin ya shafa har da wani na kusa da shugaba Putin, Oleg Deripaska, da wani mamba a kwamitin Federaliya Souleïman Kerimov wanda iyalansa ke jagorancin gungun Polyus, sai kuma Darakta janar na kamfanin Gazprom Alexeï Miller, da kuma sakatare janar na hukumar tsaron kasa, Nikolaï Patrouchev, sai kuma wasu manyan kamfanonin Rasha.
Ko a ranar 15 ga watan Maris da ya gabata, mahukuntan na Washington sun kakaba takunkumi kan wasu jami'an Rasha 15 ciki har da jami'an leken asiri.