Faransa Ta Yi Gargdi Akan Bullar Yakin Basasa A Nahiyar Turai
(last modified Tue, 17 Apr 2018 13:11:23 GMT )
Apr 17, 2018 13:11 UTC
  • Faransa Ta Yi Gargdi Akan Bullar Yakin Basasa A Nahiyar Turai

Shugaban Kasar Faransa ne ya yi gargadin saboda yadda ake kara samun sabani a tsakanin bangarorin nahiyar

Shugaba Emmanuel Macron wanda ya gabatar da jawabi a yau talata a gaban majalisar nahiyar turai ya yi ishara ya ce; Bisa la'akari da halin da ake ciki a yanzu a nahiyar ta turai da akwai nauyi da ya rataya a wuyan dukkanin jami'an nahiyar.

Macron ya yi gargadi akan sabani da banbanci da ma shakku da ake da su a tsakiyar nahiyar ta turai.

Shugaban na Faransa ya yi ishara da ficewar Birtaniya daga nahiyar ta turai, yana mai cewa shakku ya ratsa dukkanin nahiyar.

Har ila yau shugaban na kasar Faransa ya ambaci yadda wasu kasashen suke fifita zama su kadai maimakon yin imani da hadakar nahiyar turai.