EU : Yerjejeniyar Nukiliyar Iran, Na Nan Daram_ Mogherini
Babbar jami'ar diflomatsiyyar kasashen Turai, Federica Mogherini, ta ce yarjejeniyar nukiliyar Iran na Daram, kuma dole a ci gaba da kare ta.
Mogherinin na ta bayyana hakan ne a Brussels a lokacin da take amsa tambayoyin manema labarai kan makomar yarjejeniyar, bayan furicin shuwagabannin AMurka da Faransa na fatan ganin an cimma wata sabuwar yarjejeniya kan shirin nukiliyar Iran.
Kafin hakan dama kasashen turan sun nuna rarrabuwar kanuwa kan yarjejeniyar a taron ministocin harkokin wajensu a ranar 16 ga watan nan a Luxembourg.
Su dai shugaba Donald Trump na Amurka da takwaransa na Faransa Emanuel Macron sun bayyana fatansu a jiya Talata na ganin an cimma wata sabuwar yerjejeniya, matakin da Shugaban kasar Iran, Hassan Rohani ya yi fatali dashi.