Kungiyar EU Ta Sabinta Takunkumin Da Ta Kakabawa Kasar Myammar
(last modified Thu, 26 Apr 2018 19:02:53 GMT )
Apr 26, 2018 19:02 UTC
  • Kungiyar EU Ta Sabinta Takunkumin Da Ta Kakabawa Kasar Myammar

Kungiyar tarayyar Turai ta sabinta takunkumin da ta kakabawa kasar Mymmar saboda abinda ta kira da take hakin bil-adama da kasar ke ci gaba da yi.

Kamfanin dillancin labaran Reuteus ya habarta cewa  wannan alhamis, majalisar kungiyar EU ta dauki kudirin sake sabunta takunkumin sayan makamai da kuma kayayyakin da jami'an tsaro suke amfani da su.

Majalisar ta yi barazar kakabawa wasu jami'an soja da na 'yan sanda takunkumi matukar aka samu gwamnatin kasar ta Myammar da ci gaba da take hakin bil-adama.

Gwamnatin kasar Myammar ta fuskanci suka mai tsanani tare da tofin alacine daga kasashen Duniya bayan kisan kiyashin da ta yiwa al'ummar musulmin Rohinga a watan Augustan 2017 din da ya gabata.

MDD ta zarki gwamnatin Mymmar da kisan kare dangi a jahar Rakhin dake yammacin kasar,

Tun a shekarar 2012 ne dai musulmin Rohinga su ke fuskantar kisa da azabtarwa da kona gidajensu da dukiyarsu a hannun sojoji da yansanda da kuma masu tsattsauran ra'ayin addinin Buddha, irin wannan cin mutunci ya sake tasowa a karshen watan Augusta na shekarar 2017 da ya gabata, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwa da kuma jikkatar duban musulmi 'yan kabilar Rohinga tare da raba wasu duban na daba da mahalinsu.