Yarjejeniyar Nukiliya : Merkel, Na Neman Shawo Kan Trump
Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel, ta isa brinin Washigton na Amurka, inda daya daga cikin jigon ziyarar shi ne shawo kan shugaba Donald Trump akan kada ya janye kasarsa daga Yerjejeniyar nukiliyar da manyan kasashen duniya suka cimma da Iran.
Ziyarar ta Misis Merkel, na zuwa ne kwanaki uku bayan ganawar da Trump ya yi da shugaban kasar Faransa Emanuelle Macron.
Wasu Kafofin yada labarai a Jamus sun rawaito cewa ziyarar Misis Merkel a Amurkar ba tada wani armashi kamar wacce Emanuell Macron ya kai , kasancewar Jamus na adawa da suk wani yunkuri na canza fasalin yarjejeniyar nukiliyar da a aka cimma da Iran.
Jamus dai na ganin ko ba komi yarjejeniyar ta haifar da da mai ido, kuma fatali da ita, zai sa a shiga sukuwar neman mallakar makaman nukiliya a yankin.
A ziyarar da ya kai a Amurka, Shugaba Macron na Faransa ya ce yana ji a jikinsa cewa, Trump zai janye daga yarjejeniyar saboda dalilan siyasa na cikin gida.
Kawo yanzu banda Amurka, dukkan bangarorin da suka sanya hannu kan yerjejeniyar da aka cimma, da kuma masu bincike na kasa da kasa sun ce Iran na mutunta yarjejeniyar.